Tsakure:
Wannan takarda ta yi magana ne a kan yadda aka samuwar da tsohuwar kasuwar Sakkwato, yadda aka fara hada-hadar saye da sayarwa, da yadda kasuwar ta bunƙasa. Dalilin gudanar da wannan takarda shi ne tunanin da take da na cewa har zuwa yau jama’a da dama ba su san yadda aka samu tsohuwar kasuwar Sakkwato ba a matsayin wurin da ya ba ‘yan kasuwa damar haɗuwa domin gudanar da kasuwancinsu. Manufar wannan takarda shi ne yin bincike domin fito da wasu muhimman abubuwa da suka faru suka zama tushen samun tsohuwar kasuwar Sakkwato. Sakamakon da takardar ta samar shi ne lokaci mai tsawo an samu wasu ƙananan muhallai da wasu jama’a da suka daɗe suna kasuwancin wasu hajjoji da suka shafi buƙatun al’umma na gida da na waje. Domin cimma wannan manufa an samu bayanai kan muhimman wuraren kasuwanci da irin tasirinsu da yadda aka fara hada-hadar kasuwanci a wurin, da kuma irin sauyin da aka yi ta samu na kasuwanci a waɗannan wurare. An yi amfani da hanya hira da masana, tsofaffiin mutanen da suka yi kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. An yi amfani da Ra’in sauyin al’adu(Social Change theory). Ta haka aka samu bayanan da aka gudanarda wannan takarda.
DOI: 10.36349/djhs.2026.v04i01.013
author/Ibrahim Alhaji Gado
journal/Dundaye JOHS, July 2026
