Tsakure:
Wannan maƙala ta mayar da hankali ne a kan nazarin kore a sana’ar sata. Ɓarayi suna amfani da wasu dabaru su daburta hankalin mai wayo, su yi masa sata mai ban mamaki. Suna kuma yi wa kansu ɓulo, su kuɓuta idan rana ta so ta ɓatar musu. Wannan tunani ya jawo hankalin mai bincike ya gabatar da wannan maƙala. Binciken yana da manufar fito da yadda ɓarayi suke amfani da dabarar kore a wajen sata. A fito da shi ga fili jama’a su fahimce shi. Idan ɓarawo ya zo da wannan dabara, a tunatar da shi karin maganar Hausawa sa suke cewa: “Kifi yana ganinka mai jar koma.” A ƙoƙarin gabatar da wannan bincike, an yi amfani da wasu hanyoyi da suka ƙunshi tattaunawa da wasu mutane. An nazarci ayyukan masana da manazarta masu alaƙa da wannan bincike. An kuma yi amfani da hanyar ɗora aiki ta karin maganar Hausawa da suke cewa: “Mai son abin ka ya fi ka dabara.” Wannan karin magana tana nuna duk dabarun da mai kaya ya yi amfani da su domin ya kare dukiyarsa ko wata kadara tasa, ɓarawo yana da tasa dabarar da ta wuce ta mai kaya. Sakamakon binciken ya gano ɓarayi ba ƙarfi kawai suke amfani da shi ba, suna amfani da dabarar kore su dabirta hankalin mai wayo su yi masa sata..
DOI: 10.36349/djhs.2026.v04i01.012
author/Buhari Lawali
journal/Dundaye JOHS, July 2026
