Tsakure:
Sana’o’i dai wani ɓangare ne da suke nuna fasahohi da kuma hanyoyin dogaro da kai na al’umma. Wannan dalili ya sanya suka zama wasu hanyoyi da suke ƙara bunƙasa tattalin arzikin al’umma. Wannan ne ya sa suka zama sanadiyyar shaharar Hausawa a ciki da wajen ƙasar Hausa. Muradin wannan takarda ne ta dubi sana’ar gyartai ta hanyar bayyana matsayinta tare da fito da hasashen makomarta a wannan ƙarni da muke ciki na ashirin da ɗaya. Duk da cewa masana da manazarta sun gudanar da ayyuka da dama masu alaƙa da sana’o’in Hausawa, amma wannan takarda ba ta samu zarafin riskar wani aiki da ya tunkari sana’ar gyartai ba. Takardar ta yi ƙoƙarin tuntuɓar masu gudanar da sana’ar da kuma masu amfanuwa da ita, domin samun bayanai. An yi haka ne ta hanyar ziyartar su a wurin da suke gudanar da sana’arsu. Haka kuma, nazarin ya kai ziyarar rangadi kasuwanni da kuma wuraren da ake gudanar da sana’ar, saboda a fahimci ta inda salka take yin tsatsa. Sakamakon da aka gano sun haɗa da: Sana’ar gyartai ta ja baya matuƙa, saboda yawaitar kayan amfanin gida na zamani. Rashin samun kuɗin shiga mai gwaɓi daga sana’ar, yana daga cikin dalilin da ya sa take samun koma baya musamman a wannan lokaci da yanayin gudanar da harkokin rayuwa suka ƙara tsada.
Muhimman Kalmomi: Sana’a; Gyartai
DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.022
author/Ibrahim Dalha & Nasiru Muhammad Mode
journal/Dundaye JOHS, December 2025
