Tsakure:
Wannan takarda mai takenNazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da su ta hanyar ɗaukar abin da ba mutum ba su mayar da shi mutum domin su isar da saƙonsu ga jama’a ta hanyar hikima a cikin waƙoƙinsu na siyasa. A nazarin an yi amfani da waƙoƙi a ƙalla guda goma sha biyu na mawallafa daban-daban waɗanda suka yi amfani da wannan dabarar a cikin waƙoƙin. An ɗora wannan takarda bisa hanyar nazari wadda Ɗangambo (2007) ya assasa a littafinsa na Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. An yi amfani da dabaru da hanyoyin wajen gudanar da wannan nazari waɗanda suka haɗa da samo waƙoƙin daga hannun wasu mawallafan, an kuma samu waƙoƙin daga wasu kundayen bincike na ilimi a matakai daban-daban a kuma rubuce. A nazarin an gano mawallafan sun yi amfani da wannan dabarar ta hanyar yin amfani da wasu siffofi da darajoji da halaye da sauransu da mutum kaɗai aka sani da su a laƙaba wa wanda ba mutum ba ya zama mutum, domin su isar da saƙo ga masu saurare ko karatu a cikin waƙoƙinsu. Haka kuma an yi nasarar fito da ire-iren misalai na dabarar mutuntarwa ta hali da mutuntarwa ta siffa da mutuntarwa ta daraja tare da yi musu sharhi. Har ila yau kuma, ana kyautata zaton wannan nazarin zai zama jagora a kan abin da ya shafi dabarun jawo hankali musamman na mutuntarwa a waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa. Haka kuma nazarin ya zamto jagora ga manazarta da ɗalibai a ɓangaren rubutattun waƙoƙi musamman na siyasa a fannin adabin Hausa.
Muhimman Kalmomi: Mutuntarwa, waƙoƙin siyasa, mawallafa
DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.021
author/A’ishatu Isma’il Adamu & Fatima Uba Adamu
journal/Dundaye JOHS, December 2025
