Tsakure:
Wannan takarda an gudanar da ita domin fayyace da tantance
kurakurai da suka saɓa
ƙa’idojin
rubutu, da ake samu a cikin rubutun insha’in bayanin na ɗaliban Hausa. Muƙalar ta taƙaita ne ga ɗaliban
jami’ar Bauchi, Gaɗau.
An yi amfani da hanyoyi biyar na ra’in ƙalailaice kurakurai da Corder (1974) ya
samar wajen nazarin kurakuran. Tsarin samfuri na bi-maƙasudi aka bi wajen zaɓen rukunin ɗaliban domin tattara
bayanan binciken, inda aka ɗauki
ɗalibai talatin (30)
daga cikin sittin (60), sannan suka rubuta gwaji na insha’in bayani da bai gaza
kalmomi 350-500 a kan ‘Yadda Makarantarsu Take’. Har wa yau, an gudanar da
tattaunawa domin samun wasu bayanan. Takardar ta gano kurakurai a rubutun insha’in
bayanin da suka haɗa
da: rashin amfani da baƙaƙe masu lanƙwasa (kirkiri> ƙirƙir; dauke> ɗauke) wanda ya fi sauran kurakuran yawa,
sannan kuskuren haɗa
kalma a inda bai dace ba (shine> shi ne; dake> da ke), da amfani da
kalmomin Ingilishi a yayin gina jumla (lecture halls> ɗakunan karatu) da rashin
amfani da manyan harufa (gaɗau>
Gaɗau; bauchi>
Bauchi) da kuskuren rubuta kalma (sangayoyi> tsangayoyi;
mabammanta>mabambanta) da rashin daidaito na jinsi (Sa’adu Zungur jami’a ne
ta jaha> Sa’adu Zungur jami’a ce ta jaha), sannan da kuskuren jam’intawa
(Jami’ar Gaɗau ta
samar da wuraren karatu wanda ɗalibai
ke daukar karatu> Jami’ar Gaɗau
ta samar da wuraren karatu wanɗanda
ɗalibai ke ɗaukar karatu). Mafi
akasarin rashin sani da sha’awa sun taka rawa wajen musabbabin waɗannan kurakurai, sannan da
tasirin tsarin rubuce-rubuce na kafafen sada zumunta. Bibiyar littattafai na ƙa’idojin
rubutu za su taimaka wajen magance ire-iren kurakuran rubutu da ake samu a
cikin rubuce-rubucen ɗaliban
nazarin harshe, tare da yawaitar shirya bita ga ɗalibai
da marubuta a kan abin da ya shafi ƙa’idojin rubutu da nahawu.
Keɓaɓɓun kalmomi: Rubutun
Insha’i; Insha’in Bayani; Ƙa’idojin Rubutu; Kurakuran Rubutu
