Hanyoyin Nuna Gamayyar Ƙirar Kalma da Ginin Jumla a Nahawun Tsirau na Hausa

    Tsakure: 

    Wannan maƙala mai taken ‘hanyoyin nuna gamayyar ƙirar kalma da ginin jumla a nahawun tsirau a Hausa’. Maƙalace da ta tattauna a kan wasu hanyoyi da ake amfani da su wajen nuna gamayyar ƙirar kalma da ginin jumla a nahawun tsirau na Hausa. Babbar manufar wannan maƙala ita ce, fitowa da gamayyar da ake samu tsakanin ƙirar kalma da ginin jumla a ra’in kalma-sak da ra’in jumla-sak. Waɗannan ra’o’i sun samo tushe ne daga nahawun tsirau. Nahawun tsirau, wata mazhaba ce da ta ƙunshi wasu sharuɗa ko dokoki da kuma wasu alamomi da suka shafi yadda ake amfani da harshe (Halle 1962:1). Dabarun bincike da aka yi amfani da su ƙanana ne, waɗanda suka haɗa da nazarin wallafaffun ayyukan masana da manazarta, waɗanda suke bayani a kan nahawun tsirau da kalma-sak da kuma jumla-sak, waɗanda aka wallafa cikin Ingilishi. Wajen tattauna bayanan, an yi amfani da ra’in nahawun tsirau, musamman kalma-sak da jumla-sak, inda maƙalar ta gano cewa akwai wuraren da ake samun gamayya tsakanin ƙirar kalma da ginin jumla. Masu fahintar kalma-sak suna amfani da jerantawa da jagoranci da maƙwabtakar ma’ana da kuma tsarin bishiya, kamar yadda masu ra’in jumla-sak suke amfani da ƙa’idojin ginin da tsarin bishiya wurin nuna  gamayyar ƙirar kalma da ginin jumla. Wannan yana ƙara fito muna da hoton dangantakar ƙirar kalma da ginin jumla a Hausa..  

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.005

    Download the article:

    author/Isah Abdullahi Muhammad & Muhammad Sani Lawan

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages