Aron Kalmomi Daga Wasu Sassan Harsuna: Nazarin Hausar ‘Yan-tashar Mota a Garin Sakkwato

    Tsakure: 

    Manufar wannan takardar ita ce, a aiwatar da nazarin kalmomin aro a Hausar ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato. Haka kuma, takardar ta yi amfani da ra’in da ya shafi yadda mutane suke amfani da harshe ta fuskar ma’anar kalmomi, wato Ra’in Fiɗar Zantuttuka (Discourse Analysis Theory)’ wanda Harris (1952) ya assasa. Sannan, an yi amfani da hanyoyi biyu wajen tattara bayanai waxanda suka haxa da tattaunawa da kuma lura ta kai-tsaye. Takardar ta gano ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato suna sarrafa kalmomin aro wajen ambaton direbobi da yaran mota da ‘yan kamasho da ‘yan dako da fasinja da tashar mota da motoci da jami’an tsaro, ko kuma don su bayyana wani hali da suka tsinci kan su a cikin tasha ko a halin tafiya.

    Keɓaɓɓun Kalmomi: Aron Kalmomi; Hausar ‘Yan-tashar Mota; Harsuna; Sabuwar Ma’ana; Sakkwato

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.003

    Download the article:

    author/Muhammad Mustapha Umar & Yusuf Sharu

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages