Tsawon Wasali a Harshen Hausa da Harshen Ga’anda: Kamanci da Bambanci

    Tsakure: 

    Tsawon wasali wani al’amari ne da ya danganci sauya ma’anar kalmomi a harshen Hausa da harshen Ga’anda. Manufar wannan bincike ita ce, ƙara bunƙasa nazarin kwatancen harshen Hausa da harshen Ga’anda da kuma ƙara faɗaɗa nazarin sauye-sauyen sautukan harsunan a cikin ilimin tsarin sauti. An yi amfani da manya da ƙananan hanyoyi a matsayin dabarun tattara bayanan da aka gudanar da wannan bincike da su. Haka kuma, an ɗora binciken a kan Ra’in kai tsaye na yankin tsarin sauti/Ra’in haɗakar ayyukan tsawon wasali da karin sauti a harshe (Autosegmental Phonology) na Goldsmith (1976) wajen gudanar da wannan bincike, wanda ya yi bayani a kan yadda tsawon wasali yake gudana a fagen ilimin tsarin sauti. Aikin ya fito da hanyar kwatanta tsawon wasali a harsunan biyu. A taƙaice, takardar ta yi ƙoƙarin fito da kamanci da bambancin da ke akwai a tsakanin harshen Hausa da harshen Ga’anda. Binciken ya gano cewa, tsawon wasali yana wanzuwa a cikin harshen Hausa da harshen Ga’anda. Haka kuma, duka harsunan biyu sun yi tarayya da juna ta fuskar ƙwayoyin sautuka da kuma wasu nau’o’in tsawon wasali. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, ba a bambanta rubutun kalma mai ɗauke da gajere ko dogon wasali a rubutun yau da kullum na harsunan Hausa da Ga’anda, bisa dalili a wani lokaci na saukaka wa waɗanda suke karatu su fahimta.  

    Keɓaɓɓun Kalmomi: Tsawon wasali da tsarin sauti da sauye-sauyen sautuka da ma’anar kalmomi da Hausa da Ga’anda

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.006

    Download the article:

    author/Nazir Ibrahim Abbas & Ibrahim, Ismaila Girei

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages