Gudummuwar Umaru Ɗanjuma Katsina wajen Faɗakar da Al’umma: Wasan Kulɓa na Ɓarna a Faifan Nazari

    Tsakure: 

    Ayyukan adabi da dama sukan yi nuni da tsarin siyasa da zamantakewa da addini da falsafar al’umma. Don haka, marubuta adabi kan bayyana manufarsu ta hanyoyi mabambanta ta waɗannan ayyuka na adabi. Wasan kwaikwaiyo dai wani muhimmin reshe ne daga cikin rassa na adabi, kuma ta hanyar wasan kwaikwaiwo akan faɗakar da al’umma game da wasu matsaloli ko halaye mara nagarta da ta yi wa al’umma ɗaurin minti da nufin nusar da su domin a gyara gaba ɗaya. Ta haka ne wannan maƙalar ta mayar da hankali game da rawar da marubuta wasan kwaikwayo kamar Umaru Danjuma Katsina ke takawa don ganin al’umma sun faɗaku game da wasu matsaloli da suka yi musu katutu. Nazarin gundarin saƙon littafinsa na Kulɓa Na Ɓarna (wato Content Analysis) shi ne abin da ya yi jagora wajen fito da rawar da marubuta wasan kwaikwayo ke takawa wajen faɗakar da al’umma game da wasu illoli da ke damfare a cikin al’umma don su guje masu. Daga ƙarshe, an ɗora wannan bincike a kan ra’in gudunmuwar adabi ga al’umma domin nuni da gudummuwar da marubuta adabi ke badawa wajen wayar wa al’umma kai.  

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.019

    Download the article:

    author/Bala Abdullahi & Galadima Mubarak Soba

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages