Tsakure:
Wannan takarda mai taken Gargaɗi a cikin waƙar Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya: Madogara daga wasu Nassoshin Addinin Musulunci, ta yi bayani ne a kan irin dangantakar da take tsakanin tsoratarwa da hani da addini ya yi a kan aikata munanan ɗabi’u, da faɗakarwar da jan kunne da marubucin waƙar ya yi wa Hausawa na yankin Arewacin Najeriya a kan wasu ɗabi’u marasa kyau da suke aikatawa. Daga cikin munanan ɗabi’un da binciken ya gano akwai rashin mai da hankali wajen neman ilimi da taɓarɓarewar tarbiya da kawalci da almubazzaranci da gulma da hassada da baƙin ciki da cin amana da camfi da ƙarya da roƙo da fariya da sauransu. Binciken ya gano cewa tabbas akwai dangantaka mai ƙarfi dangane da shawarar da marubucin waƙar ya ba wa ‘yan arewa a kan wasu ayyuka marasa kyau da suke aikatawa da kuma hani da tsoratarwar da Al’ƙur’ani da Hadisai suka yi a kan aikata aiyuka marasa kyau. Wannan waƙa da aka nazarta an same ta ne a cikin littafin marubucin da ya kira “Waƙoƙin Sa’adu Zungur” (1968) littafi ne da yake ƙunshe da waƙoƙi ciki har da ita wannar waƙar. sannan aka sake rubuta ta domin yin wannan bincike. Haka kuma an karanta ta da yawa domin ƙara fahimtar komai. An yi amfani da Ra’in fanɗarewa daga karɓaɓɓun Al’adun A’umma (Deviance theory) aka ɗora takardar a kansa. Ra’in yana bayani ne a kan yanayi na fanɗarewa daga al’adar da al’umma ta saba da ita. Mutum na iya fanɗarewa ta hanyar ƙin aikata wasu al’adu ko wuce gona da iri a wajen aikata al’adu ko ma aikata al’adun da ba su yi daidai da dokokin da al’ummar da yake ciki ba. (Otite and Ogionwo 1981:217).
DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.018
author/Ayagi, J.S., Musa, I.I. & Dayyabu, A.
journal/Dundaye JOHS, December 2025
