Tsakure:
Masu azancin magana kan ce ‘‘Kowane tsuntsu; kukan gidansu yake yi’’. Malaman zaure mutane ne waɗanda suke koyar da al’umma ilimin addinin Musulunci a fannoni daban-daban, domin su fahimci addini kamar yadda ya kamata, musamman karatun Alƙur’ani maigirma da waɗansu ilmuka. Manufar wannan binciken ita ce nazartar kalmomi da yankin jumloli da kuma jumlolin da malaman zaure suke amfani da su a wajen hulɗa da mu’amalarsu da ɗalibai da kuma al’umma. Saboda maganganunsu da zantukansu na sadarwa sun bambanta da na gama-gari. An ɗora binciken bisa ra’in Greenberg (1962) da yake cewa ‘‘Hulɗa tsakanin harsuna, yana nufin tasirin harsuna a kan juna’’. Yakasai (2005) ya tabbatar da wannan ra’in, a inda ya ƙara da cewa ‘‘akwai tasiri da hulɗa, kana akwai tasiri babu hulɗa kaitsaye’’. An yi amfani da hanyoyin tattara bayanai manya da ƙanana. An yi amfani da hanyar zuwa da kai ya fi aike, wato ziyara a wasu Zaurukan karatu da majalisan karatu da kuma sauraren kafafen zamani na sada zumunta. Waɗanda suka haɗa da karatukan da aka naɗa da memori (memory). Sakamakon bincike ya nuna akwai Hausar rukuni ta malaman zaure ta kalma da yankin jumla da jumla. Misali a kalma, yankin jumla da kuma jumla. Da wannan ne Hausawa kan ce ‘‘A san mutum a san sana’arsa ko Kowa bar gida, gida ya bar shi”.
DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.017
author/Buhari Aiku Gwandu
journal/Dundaye JOHS, December 2025
