Nazarin Tsarin Rubuta Gajeren Saƙo da Hausa a Kafafen Sadarwa na Zamani

    Tsakure: 

    Wannan takardar ta yi nazari ne akan tsarin rubutun Hausa da ake yi a kafafen sadarwa na zamani da suka samar da sabon salon rubutun Hausa da ake rubuta kalmomi a taƙaice ta hanyar gajarta rubutun saƙo a kafafen sadarwa na zamani da aka yi nazarinsu a wannan aikin. Manufar nazarin shi ne na ya ilimantar da ma’abota waɗannan kafafe yadda ya kamata a bi ƙa’idojin rubutun Hausa da amfani da harufan da Hausa take da su domin gyara rubutun da ake yi a irin waɗannan kafafe na sadarwar zamani. An nazarci wasu saƙonni da aka rubuta da Hausa a shafukan fezbuk (Facebook) da was‘Af (WhatsApp) wanda sakamakon nazarin ya nuna yadda ake amfani da wani irin salon rubutun Ingilishi wanda ya saɓa ƙa’idojin rubutun Hausa da take da su. An yi amfani da ra’in Alamomin Rayuwar Al’umma na mazhabar Saussure (1978) wanda ya jagoranci nazarin da aka yi. Daga ƙarshe an kawo shawarwarin yadda za a yi rubutun Hausa ta amfani da harufan Hausa masu ƙugiya da masu goyo waɗanda Hausa take da su a tsarin rubutunta. 

    Muhimman kalmomi: amfani, tsari, kafafe, shafuka da salo

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.002

    Download the article:

    author/Muhammad Sani Umar Kulumbu

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages