Tsakure:
Yaƙi da zaman lafiya kishiyoyin juna ne. Yanaye-yanaye ne na zamantakewar rayuwa. idan al’umma ta yi yawa, akan sami bambancin ra’ayoyi. Ba abin mamaki ba ne ga samun bambancin ra’ayoyi tsakanin al’ummomin da ke zaune a muhalli guda da kuma masu maƙwabtaka da juna. Duk inda rashin jituwa ya ɓulla, lallai ƙarshensa yaƙi ne. Idan aka gwabza, kowa ya ji kowa, sai kuma a dawo a yi sulhu wato a yafe wa juna. Da zaran an yafe wa juna aka manta da baya, sai kuma zumunci mai danƙo ya biyo baya a narke a koma wasa. Wannan zumunci mai danƙo shi ake kira zaman lafiya. Ke nan, da zaman lafiya da yaƙi taubasai ne. Wannan maƙala mai taken, “Yaƙe-Yaƙe da Zaman Lafiya a Cikin Littafin Magana Jari Ce,” sharhi ne dangane da matsayin yaƙe-yaƙe da zaman lafiya da yadda suka zama furen kallo ga marubuta labaran Hausa. An yi garkuwa da littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam. Ke nan maƙalar za ta bayyana yadda yaƙi da zaman lafiya suka zama wasu saƙonni na musamman a cikin littafin na Magana Jari Ce. An karanta littafin Magana Jari Ce da wasu ayyuka na masana, waɗanda suka yi sharhi a kan yaƙi da zaman lafiya, a matsayin manyan hanyoyin da aka bi aka gudanar da binciken. An yi amfani da ra’in karin maganar nan mai cewa, “Idan An Ciza, Sai a Hura” a wajen gudanar da maƙalar. Daga ƙarshe sai maƙalar ta gano cewa yaƙi da zaman lafiya su ne ma manyan ginshiƙan da aka gina littafin Magana Jari Ce da su. Haka kuma, mawallafin ya yi amfani da littafin na Magana Jari Ce don ya nusar da al’umma a kan dalilan da kan haddasa yaƙi, domin a yi taka-tsan-tsan da su da kuma yadda ake tattalin dawo da zaman lafiya idan ya kuɓuce..
Fitilun Kalmomi: Yaƙe-yaƙe, Zaman Lafiya, Magana Jari Ceauthor/Atuwo, A.A. and Faruk, A.
journal/GNSWH, April 2024