Habaici Cikin Waƙar “Kowa Ya Yi Maka Kan Kara” Ta Alhaji Garba Gashuwa

    Tsakure: 

    Wannan nazari mai suna “Habaici Cikin Waƙar Kowa Ya Yi Maka Kan Kara ta Alhaji Garba Gashuwa. Babbar manufar nazarin ita ce fito da habaici ta hanyar zaƙulo ire-iren hikimomi da basirori da dabaru na sarrafa harshe da mawallafin ya yi amfani da su a cikin waƙar domin ya jawo hankulan jamaa zuwa ga manufa. An kalli yadda marubucin ya yi amfani da dabarar sanya habaici a waƙar cikin hikima domin ya isar da saƙonsa. An ɗora wannan nazari a bisa mazahabar Abdulƙadir Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙar daga hannun marubucin a kuma rubuce tare da tattaunawa da shi. A nazarin kuma an gano marubucin ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe ta sanya habaici a cikin waƙar don ya mayar da martani ga abokin adawa. Gudunmawar da nazarin ya bayar ita ce zai zama jagora ga manazarta da ɗalibai ta yadda za su nazarci habaici a rubutacciyar waƙa, musamman waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa.

    Fitilun Kalmomi: Salo, Habaici, Waƙoƙin Hausa, Alhaji Garba Gashuwa, Sarrafa harshe

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.018

    Download the article:

    author/Adamu, A.I. and Buhari, A.T.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages