Tsakure:
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin yin bitar wasu matsaloli a al’umar Hausawa waɗanda suke haddasa yawaitar mutuwar aure. Waɗannan matsaloli kamar yadda aka yi nazarinsu, suna da alaƙa ne da zamani. Wato idan aka kwatanta, za a ga a da ba haka rayuwar ta Hausawa take ba. An sami tattara waɗannan bayanai ne ta bin bahasin dalilan mutuwar aurarrakin daga bakin zawarawan da abin ya shafa da kuma mazan da suka yi sakin. Haka kuma an sami wasu bayanan daga dangin waɗanda abin ya shafa da bayanan kotu da na kafafen yaɗa labarai musamman na sadar da zumunta na zamani. Nazarin ya gano cewa, wasu daga cikin matsalolin da suke jawo yawaitar mutuwar aure sun samu ne daga matan. Wasu kuma suna da alaƙa da mazan. Wasu sun shafi dangi ko iyaye na ma’auratan, a yayin da aka ɗora alhakin wasu matsalolin ga gurɓacewar al’uma wadda sauyawar zamani ya kawo. Nazarin ya gano cewa, akwai illoli masu yawa da al’umar Hausawa za ta fuskanta idan aurarraki suka ci gaba da mutuwa kamar yadda abin yake ƙaruwa a wannan zamani.
Fitilun Kalmomi: Matsaloli, Al’umar Hausawa, Mutuwar aure, Ƙarni na 21
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.016
author/Ibrahim Sarkin Sudan Abdullahi
journal/GNSWH, April 2024