Tsakure:
Wannan aiki yana ƙunshe da bayanai dangane da yadda mawallafiya ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ta yaɗa wasu al’adun Hausawa da kuma na wasu al’ummomin da ba Hausawa ba. Sannan ta yi amfani da wannan dabara domin ta yaɗa addinin Musulunci, da kuma yanayin zamantakewar iyali a gidajen Hausawa. Aikin bai tsaya nan ba, sai da ya taɓo yadda mawallafiyar ta yi amfani da dabarar domin ta yaɗa tattalin arziki irin na ƙasar Hausa, ta yadda wasu maza da mata suke gudanar da wasu sana’o’in.
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.007
author/Balarabe Zulyadaini & Yusufu Suleiman
journal/GNSWH, April 2024