Tsakure:
Confucius masanin falsafar nan na ƙasar Sin, shi ne ya bayyana adabi a matsayin rumbu na hikima. Ya faɗi haka ne a lokacin da yake nazarin irin dangantakar da take tsakanin adabi da hikima da kuma ƙumshiyar kowanne domin ci gaban al’umma. Wen tana nufin ƙirƙirarrun ayyukan adabi, a yayin da dao take nufin hikimomin da suke ƙumshe a cikin irin waɗannan ayyuka. Marubutan ƙasar Sin sun yi ittifaƙi cewa adabi rumbu ne na hikima, tamkar mota ce mai ɗauke da kaya. Wato hikima ita ce kayan da babu mai ɗaukarsu face adabi. Ƙumshiyar wannan maƙala ita ce tsokaci a kan matsayin waƙa a adabin Sinawa. Domin cimma wannan manufa, an karkasa maƙalar gida biyar. Kashi na farko da na ƙarshe, shimfiɗa ce da naɗewa. A kashi na biyu an waiwayi ma’anar waƙa da karin waƙa da zubi da tsari cikin yabo da zambo da kuma matsayin waƙoƙi gama-gari. Kashi na uku kuwa ya taɓo ƙa’idojin rubutun zube ne da waƙa, wato fasaha a cikin manufofin waƙa da kuma amfani da adon harshe a waƙa. Kashi na huɗu misalai ne na yanaye-yanaye da waƙoƙi sukan bijiro kamar saƙon zuci da kaɗaici da baƙin ciki da kishin zuci da kuma tarihin al’umma.
Fitilun Kalmomi: adabi, Sinawa, hikimomi, waƙoƙi, ƙa’idojin rubutun
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.006
author/Salisu Ahmad Yakasai FLAN
journal/GNSWH, April 2024