Tsakure:
Zamfarawa wani sashe ne a cikin al’ummar Hausawa waɗanda suka kasance da hasaloli kyawawa cike da halayen kirki tare da aiwatar gaskiya da son ‘yan’uwa da kuma abokai. Mutane ne masu kunya, masu kawar da kai, sannan kuma masu neman shawarwari a tsarin hasalolin rayuwa. Zamfarawa mutane ne, masu kulawa, waɗanda suke iya zama da kowaɗanne nau’o’in mutane da suka sami kansu a cikinsu ne. Suna tafiyar da kyawawan mu’amaloli ne da mutane daban-daban, musamman idan aka yi la’akari da yanayin harkokinsu da mutanen Legas da na Ibadan da na Ogbomosho da na Ghana da na Paris da na Ingila da na Amurka da na Libya da na Agadaz da na Anambara da na Adamawa da na Zuru da na Yawuri da na Argungu da na Kano da na Katsina da na Zariya da dai sauransu. An ayyana, ayyuka ne da hidimomin rayuwa suka kawo Zamfarawa jihar Kano. An fahimci Zamfarawa mazauna Kano sun haɗu ne a sigar mutuntawa tare da girmama duk wani jinsi na ɗan’adam da suke zaune da shi. Hakan ne kuma ya haddasa musu aiwatar da wani yunƙuri tare da azama na kafawa da samar da Ƙungiyar Zamfarawa Mazauna Jihar Kano kwata. Daga cikin manufofin da suka haddasa kafa wannan ƙungiya bai wuce a ƙara samar da danƙon zumunci ba, tare da lura da ɗorewar kulawa da juna. Haka kuma yana daga cikin manufofinta, a ƙara saka ƙaimi wajen taimakawa da ƙarfafawa juna da kuma abokan hulɗa, tare da lazimtar aikata halaye na gari da ƙarfafa ayyukan addinin Musulunci da bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa dukkan nau’o’i da rassa na ilimi da kuma kulawa da sa-hannun ƙungiya wajen samar da ayyukan-yi ga matasa. Ta haka ake ba da shawara da a bunƙasa wasu muhimman gurabu domin a aiwatar da hidimomin ƙungiyar. Sannan, gurabun kar su yawaita; a zaɓi mutanen da suka dace a ɗora su a matsayin Shugaban Ƙungiya da Sakataren Dauwana Ayyukan Ƙungiya da Sakataren Tantance Shiga-da-Ficen Kuɗin Ƙungiya da Ma’aji da Sakataren Sadar da Ayyukan Ƙungiya. Sannan a samar da Kundin Tsarin Mulki (Constitution) da Kwamitin Amintattun Wakilai na Ƙungiya da Kwamitin Iyayen Ƙungiya da kuma Kwamitin Lauyoyin Ƙungiya.
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.008
Fitilun Kalmomi: tambihi, tunasarwa, zumunci, zamfarawa, mazauna jihar kano
author/Sa’idu Muhammad Gusau
journal/GNSWH, April 2024