Gabatarwa
Jawabin shimfiɗa Buzun Karatu (Inaugural Lecture) wata irin gagarumar hidima ce a tsarin karatu, da koyarwa, da bincike, da renon ɗaliban ilmi, Jami’o’i da cibiyoyin bincike. Buki ne na nuna wa gwarajen da suka yi fice a fannoni daban-daban na ilmi. Maƙasudinsa, suna Jami’a ya yi zara; a duniyar ilmi, sunan Tsangaya ya yi fice a farfajiyar Jami’a, Sashe ya yi kere cikin takwarorinsa. A ɓangaren wanda aka yi bukin dominsa, wata dama ce ta tabbata, cewa, ba a wane bakin banza; tabbas! Zomo ba ya kamuwa daga zaune; wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokuwa. Sanin kumbo kamar kayanta, na zaɓi , raɗa wa wannan jawabi suna: “Sannu ba ta hana zuwa ko za a daɗe ba a kai ba.” Na ɗora binciken wannan ɗan jawabi a kan wata fatawa ta Sani Aliyu Ɗandawo da ke cewa:
Jagora: Tafiya sannu-sannu
sai giwa,
Yara: Ina waɗanga masu gaugawa.
Gindi: Shehu sauran
mazan farko,