Nuta Cikin Tarihin Alƙalin Lardin Sakkwato Mallam Yahya Nawawi (1897-1979)

    Tsakure: 

    Tunanin shirya wani kundi wanda zai ƙunshi maƙalu na ilmi domin ciyar da bincike gaba, musamman kan adabin Hausa ya taso ne a wani zaman liyafar cin abinci da aka yi a harabar Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato ranar 15 ga Maris,` 2023 daga ƙarfe 7-10 na dare. Wannan liyafa an shirya ta ne domin karramawa ga Farfesa Abdullahi Bayero Yahya. Shi kuma Farfesa Abdullahi Bayero ya cika shekaru saba’in a wannan lokaci saboda haka ya rubuta takardar aje aikin jami’a a matsayin mai ritaya. Wannan nasara ta cimma shekaru saba’in da yin ritaya, ita ce dalilin shirya walima domin girmamawa da taya murna gare shi. Wannan kuma ita ce damar da na samu na shiga sahun sauran ɗalibai wajen rubuta muƙala kamar yadda hakan ta kasance.

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.002

    Download the article:

    author/Aliyah Adamu Ahmad (Mrs)

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages