Tsakure:
Waƙa kamar yadda masana suka yi ta ƙoƙarin bayyanawa zance ne da ya saɓa da zance na yau da kullum domin ita shiryayyiyar magana ce mai ƙunshe da saƙo wadda ake aiwatarwa cikin hikima da balagar harshe ta hanyar zaɓen kalmomi da shirya su tare da sadar da su a kan wasu ƙa’idoji. Salo a cikin ayyukan adabi yakan kasance wata gada ce wadda ta kanta ne fasihi ke bi ya gwada ƙwanjin fasaharsa da baiwarsa ta mallakar harshe tare da samun damar isar da saƙonsa cikin sauƙi da burgewa. Masana irin su Leech (1968) da Yahaya (2001) da Garba (2014) sun tabbatar da cewa iya sarrafa salon fasihi shi zai ba shi dama ya samar da waƙa mai daɗi da armashi kuma har mutane su kwaɗaitu da waƙar tasa. Masana irin su Mukhtar (2001) da Yahaya (2001) da Adamu (2002) suna kallon salo a matsayin wani faffaɗan fage na nazari wanda kusan a iya cewa ba shi da iyaka amma duk da haka ana nazarinsa ta fuskar harshe da kuma adabi.Wannan maƙala ta yi nazarin yadda Alhaji Sani Sabulu Kanoma ya sarrafa salailai mabambanta ne a cikin waƙarsa ta ‘Salo’ musamman ta fuskar adabi, domin kuwa ba ta taɓo abin da ya shafi harshe ba. Maƙalar ta yi dubi ne na ƙwaƙƙwafi tare da ƙwanƙance ɗiyan waƙar da ƙoƙarin fayyace su a kan wani nau’i na salo. A wajen tattaro bayanai, maƙalar ta juyi wannan waƙa ta ‘Salo’ a rubuce, sannan ta bibiyi bayanan masana a kan salo da hanyoyin nazarinsa waɗanda suka zamar mata matashiya wajen ganin an zaƙulo nau’o’in salalai da makaɗin ya sarrafa a cikin waƙar. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da cewa makaɗin gwani ne wajen iya sarrafa salo wanda hakan ya sa waƙoƙinsa suka samu karɓuwa a wurin mutane kuma har duniya ta sansa a matsayin fitaccen makaɗi mai ɗimbin hikima sannan kuma waƙoƙin nasa suka ɗauki tsawon lokaci ana sauraren su ba tare da sun ɓace ba duk kuwa da cewa makaɗin ya daɗe da barin duniya.
Fitilun Kalmomi: Adabi, waƙa, Salo Sani Sabulu
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.032
author/Rabiu Bashir
journal/GNSWH, April 2024