Tsakure:
Danganataka a tsakanin gidajen rediyo da waƙoƙin baka abu ce da ta daɗe a ƙasar Hausa. A kan haka ne wannan takarda ta ƙudiri anniyar binciko matsayin Alhaji Mamman Shata da waƙoƙinsa a wasu fitattun gidajen rediyo. An yi wannan binciken ne ta hanya lura da shirye-shiryen gidajen rediyon inda aka taskace shiraruwa guda ashirin da ake samun shata da waƙoƙinsa a cikinsu. Haka kuma an nazarci ayyukan da suka shafi shata da rayuwarsa ta waƙa. A ƙarshe takardar ta gano irin yadda aka samar da rediyo a nahiyar Afirka da Najieriya da Arewacin Najeriya da yadda rediyon ya tasirantu da waƙoƙin Hausa. Mun ga yadda aka tabbatar da kasantuwar waƙoƙin Shata tun kafin kafuwar gidan rediyo a ƙasar Hausa da yadda rediyon ya ƙara yaɗa waƙoƙin Shata.Bugu da ƙari, an fito da irin shirye-shiryen rediyo da ke gabatar da waƙoƙin Shata kacokan da ma waɗanda waƙoƙin nasa kan fito tare da na wasu mawaƙan. Wani muhimmin abu da wannan takarda ta fito da shi fili shi ne irin gudunmawar da rediyo ke bayarwa wajen adana da taskace waƙoƙi. Euba (1976:29) ya tantace rediyo a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin taskace waƙoƙi.
Fitilun Kalmomi: Alhaji Mamman Shata, Shirye-shirye, Gidajen rediyo
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.033
author/Sabi’u Alhaji Garba
journal/GNSWH, April 2024