Tsakure:
Nazarin karin harshe wani ɓangare ne a cikin nazarin harshe wanda yake ƙoƙarin kwatanta nau’o’in kare-karen harshe masu kusanci da juna ta kammani tare da fitowa da wuraren da suke da bambanci. Wannan fagen ya fi sha’awa da alaƙar da ake samu tsakanin kare-karen harshe bisa ga bambance-bambancen da ake samu tsakaninsu, domin alaƙar itace take taimakawa wajen fahimtar juna tsakanin masu magana da kare-karen harshe na harshe ɗaya. Malamai masu nazarin karin harshen Hausa sun rarraba kare-karen harshen Hausa na yanki a manyan yankuna na Gabas da na Yamma. Malaman sun yi wannan rabon ne ta la’akari da muhalli da kuma kamannin kare-karen harshen ta fuskar nahawu ko siffofin harshe. Ana iya auna bambancin karin harshen Hausa na yanki a dukkan matakan nazari na nahawu tun daga; gundarin sauti da tsarin sauti da ƙirar kalma da ginin jumla da kuma ma’ana (ta kalmomi). Wannan bincike ya ta’allaƙa ne ga karin harshen Hausa na Yamma. Hanyoyin ƙirar kalma da wannan bincike ya gano ana amfani da su su ne na; kumbura da ƙirƙira da kuma ninki. Manufar binciken ita ce,fito da wasu siffofin ƙirar kalma na Hausar Yamma, wato hanyoyin da ake bi wajen samar da kalmomi a Hausar Yamma. Hausar Yamma a wannan nazari ta ƙunshi kare-karen harshen da ake samu a Yammacin ƙasar Hausa na; Sakkwatanci da Zamfarci da Kabanci da Arauci da Gobirci da kuma Adarci. An samu bayanan da aka gudanar da wannan binciken bayan gudanar da bincike a cikin al’ummomin da suke zaune a waɗannan yankunan ta hanyar shirya takardar amsa tambaya da kuma hira da tattaunawa da aka ɗauki zantukan mutane daban-daban a rubuta da kuma waɗanda aka naɗa ta rikoda.
Fitilun Kalmomi: Ƙirar kalma, Hausar yamma, Karin harshe, Daidaitacciyar Hausa, Ƙwayoyin ma’ana
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.031
author/Nazir Ibrahim Abbas
journal/GNSWH, April 2024