Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Mabuɗin Nazari da Binciken Adabin Hausa: Wani Ɗan Yayyafi a Cikin Gudunmuwarsa

    Tsakure: 

    Da zarar mai Nazarin waƙa ya tashi yin wata waƙa yakan mayar da hankalinsa kacokan ta yin ƙoƙarin lalubo tubalan da aka gina wannan waƙa, wato zubinta da saƙonta/jigo da kuma gano ire-iren salailan da mawaƙin ya bi don isar da saƙonsa zuwa ga waɗanda yake nufi da shirya waƙarsa. A wani lokacin ma, manazarcin kan so ya haɗa aikinsa da ba da ma’anar waƙa gabaɗaya da ambatar rabe-raben waƙar Hausa, (wato waƙar ta baka ce ko kuwa rubutatta ce), har ma da zaƙulo tarihin samuwar waƙar Hausa gaba ɗaya. Zai yi ƙoƙarin dukkan waɗannan abubuwa kafin ya shiga jan aikin feɗe waƙar. Dukkan waɗannan bayanai da suka gabata na matakan nazarin waƙa, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya, ya yi cikakkiyar shimfiɗa a wani hoɓɓasa da ya gudanar don share wa manazarta hawaye da ire-iren makamai da hanyoyi da shawarwari da ya kamata a bi, don a gano bakin zaren gudanar da bincike. ya tsara hakan ne musamman a cikin wasu shahararrun litattafansa da ya wallafa don manazarta da marubuta waƙoƙin Hausa, wato littafin ‘Jigon Nazarin Waƙa 1997’ da kuma littafin ‘Salo Asirin Waƙa 2001 da 2006’. Ga kuma wasu ɗimbin takardu na adabi da ya gabatar a ire-iren taruka daban-daban da aka gudanar na ilmi da kuma wasu da dama da aka wallafa a cikin mujallu na cikin gida da kuma na ƙasashen waje. Duka dai don ya share wa manazarta waƙoƙin Hausa hawaye ga ire-iren hanyoyi da za su iya bi, don samun sauƙin gudanar da ayyukansu ba tare da zubar da hawayen ba. Wannan takarda za ta fi karkata ne da kandamin littafinsa, wato Jigon Nazarin Waƙa. Kafin ci gaba da bayanai yana da kyau, kada a yi tuya a manta da albasa kafin tattauna ɗumbin gudunmuwar da wannan Shaihin Malamin ya bayar, bari a fara da ambaton wani ɗan bayani ƙyas game da tarihin wannan bawan Allah a Gabatarwar wannan takarda.

    Fitilun Kalmomi: Abdullahi Bayero Yahya, Rubutaccciyar Waƙa, Salo, Jigo


    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.003

    Download the article:

    author/Hamza Alhaji Ainu

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages