Tsakure:
Hanyoyin sadarwa domin isar da saƙonni sun kasu kasha daban-daban musamman idan aka yi la’akari da yanayin yadda akan sarrafa hanyoyin da kuma yanayin waɗanda akan isar wa saƙonnin. Karin Magana kuwa, wata hanya ce da akan yi amfani da wasu kalmomi don isar da saƙonni na musamman ga masu saurare. Wannan maƙalar za ta kalli yadda Girafiti ya kutsa cikin karin maganar Hausa, da yadda ake iya ganin shan-ruwan-tsuntsayen da yakan yi a cikin Karin maganar Hausa. Bibiyar Karin maganar Hausa da sauraren yadda akan sarrafa su, su ne hanyoyin da wannan maƙalar ta bi domin tattaro bayanan da aka kawo. Don haka, don samun gudanar da wannan maƙalar kamar yadda ya kamata, an kawo gabatarwar aikin da ma’anar girafiti da kuma tsokaci game da ma’anar karin magana. Sannan maƙalar ta kawo wasu wuraren da girafiti ya kutsa a cikin karin maganar Hausa tare da misalai. Sai kuma sakamakon bincike da kammalawa.A ƙarshe maƙalar ta gano cewa, a karin maganar Hausa akwai tasirin girafiti da akan samu jefi-jefi.
Fitilun Kalmomi: Sadarwa, Harshen Hausa, Girafiti, Karin magana
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.025
author/Abdullahi Yunusa
journal/GNSWH, April 2024