Tarihin Alaƙar Birnin Zauma da Zamfarawan Gummi

    Tsakure: 

    Dangantaka a tsakanin kafuwar garuruwa da birnane abu ce mai dogon tahiri a ƙasar Hausa. A kan haka ne wannan muƙala ta himmatu wajen tono irin alaƙar da ke tsakanin mutanen da suka kafa birnin Zauma da kuma masarautar Gummi dukkansu a jihar Zamfara. An yi amfani da dabarun bincike irin na tuntu~ar masana asalin kafuwar garuruwan da masarautun. Yin amfani da wannan dabarar ya taimaka ainun wajen samar da ingantuttun bayanai daga tsofaffi da masu ruwa da tsaki a sanin alaƙar garuruwan. Wata dabara da aka yi amfani da ita kuwa, ta haɗa da nazarce-nazarcen littaffai da suka bayyana matsayin garuruwan guda biyu. A ƙarshe muƙalar ta gano yadda Zamfarawan Gummi suka samo asali daga Tumfafi ta ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, waɗanda suka yi hijira zuwa garin Birnin zauma, daga bisani zuri’ar suka mamaye garin Gummi da masarautar gaba ɗaya.

    Fitilun Kalmomi: Alaƙa, Birnin Zauma, Zamfarawa, Masarautar Gummi

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.024

    Download the article:

    author/Abdullahi Sarkin Gulbi, A. Musa, S.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages