Kirari a Wasu Waƙoƙin Makaɗan Maza

    Tsakure: 

    Wannan takarda mai suna “kirari a wasu waƙoƙin makaɗan maza” ta ƙunshi ma’anar kirari daga masana daban-daban, da rabe-raben kirari tare da fito da yanayinsa da sigoginsa da kuma yadda yake yin naso a cikin wasu waƙoƙin makaɗan maza. A yayin rubuta takardar an bi waɗannan watau bibiyar wasu daga cikin bugaggun littattafai waɗanda masana suka rubuta domin fito da misalai. Haka kuma a takardar an kawo wasu sigogin kirari guda biyar (5) da makaɗan maza kan yi amfani da su wajen gina waƙoƙinsu na kirari, waɗanda suka haɗa da kirari da sigar yin zuga da kirari ta sigar nuna jarumta, da kirari ta sigar nuna bajinta da kirari ta sigar siffantawa da kuma kirari ta sigar yin yabo. Daga ƙarshe an kawo kammalawa da manazarta.

    Fitilun Kalmomi: Kirari, Waƙoƙi, Makaɗan Maza

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.026

    Download the article:

    author/Buhari, A.T. and Usman, H.A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages