“In Ka Ƙi Ji Ba Ka Ƙi Gani Ba”: Nazarin Mummunan Ƙarshe ga Masu Miyagun Halaye a Cikin Wasu Fina-finan Hausa

    Tsakure

    Mummunan ƙarshe, wani ɓangare wanda rayuwa kan samu kanta a ciki a sanadiyyar aikata wani mugun hali, lokacin gudanar da rayuwar da ta gabata. Wannan na iya kasancewa a bayyane cikin zahiri ko a fina-finai. Wannan takarda ta waiwayi yadda fina-finan Hausa a matsayinsu na wasan kwaikwayo sukan fito da mummunan ƙarshe ga mutanen da suke aikata miyagun halaye a cikin tsarin fim. An yi sharhin fina-finan tare da nuna yadda ƙumshiyarsu take cike da kwaikwayon halayyar mutane kai tsaye ko a kaikaice domin isar da saƙo ga alumma. Bugu da ƙari, takardar ta nuna yadda waɗannan fina-finai sukan ilmantar ta hanyar yin gargaɗi da kashedi da hannunka mai sanda ga al’umma domin su guje wa aikata miyagun ayyuka da nufin kauce wa aukawa cikin mummunan ƙarshe.

    Fitilun Kalmomi: Mummunan Ƙarshe, Miyagun Halaye, Fina-finan Hausa

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.064

    Download the article:

    author/Aishatu Yahaya Tambawal

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages