Tsakure:
Marubuta waƙoƙin Hausa kan yi amfani da siffar tatsuniya a cikin waƙoƙinsu domin kawo nishaɗi, da wurin faɗakarwa da ilmantarwa. Haka kuma a waɗansu lokuta sukan riƙa bayyana halayyar rayuwar mutane a cikin waƙa ta hanyar sanya muhallin tatsuniya don bayyana hoton rayuwa a cikin bayani. Abin sha’awa tattare da wannan, shi ne a kan sami marubucin waƙa ya shirya waƙarsa domin ilmantarwa ko nishaɗi ko faɗakarwa sai a ci karo da tun a farkon waƙar ya tsara ta cikin sigar tatsuniya ko kuma cikin waƙar sai a ci karo da wasu baitoci da ke ɗauke da sigar tatsuniya.
Fitilun Kalmomi: Tatsuniya, Mawaƙa, Siffofi da Muhallai, Rubutattun Waƙoƙi
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.063
author/Anka, Y.H. and Jangebe, S.A.
journal/GNSWH, April 2024