Tsakure
Yabo na cikin manyan turakun da makaɗan baka suka fi yawaita yin waƙoƙi na baka a kan sa. Kusan shi ne ma fitaccen turken waƙoƙin baka na Hausa domin mafi yawan waƙoƙin manufofinsu sukan kasance yabon waɗanda ake yi wa su ne. wajen tsara Wannan takarda an yi amfani da muhimman hanyoyi wajen tattaro bayanan da suka dace da suka haɗa da sauraron waƙoƙin da kuma duba maƙalu da mujallu da kuma sauran rubuce-rubuce. A ƙarshe nazarin ya gano cewa makaɗa Mamman Shata ya yi wa mata da yawa waƙa, musamman domin nuna yabo a gare su a ƙoƙarin fitowa da halayensu na kyauta ko bayyana asalinsu ko zati da kyawon halitta..
Fitilun Kalmomi: Ƙananan Tubalai, Turken Yabo, Mata, Waƙoƙin Shata
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.065
author/Rabiʼatu Abubakar Umar
journal/GNSWH, April 2024