Salon Amfani da Karin Magana a Waƙa Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari Daga Wasu Rubutattun Waƙoƙin Hausa

    Tsakure: 

    Salon amfani da karin magana a waƙoƙin Hausa na baka, ko rubutattu, wani tsalli ne daga cikin salailan da Yahya, (2001 da 2016), ya bayyana, ya kuma tsattsefe shi tare da zaratan misalai. A wannan takarda an dubi wannan salo na amfani da karin magana, kamar yadda ya kawo shi, kana aka yi nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa, sannan aka ɗora nazarin bisa wannan fahimta ta Shehin Malamin. A fahimtar masanin, ya ce marubuta waƙoƙin Hausa suna amfani da karin magana ta hanyoyi guda uku da ya haɗa da faɗaɗa karin magana, da gutsure karin magana da kuma ƙirƙirar karin magana. Har ila yau, sai ya nuna cewa dukkan karin maganar da ake amfani da ita a waƙa ana yi ne ko dai don yin ishara, ko ƙarin bayani ko nuna ƙwarewa a harshen, ko kuma adana karin maganar. An zaƙulo misalai daga waƙoƙinHausa da suke nuni ga faɗa ta wannan masani, kuma Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, ta hanyar amfani da dabarar bincike ta bibiyar rubutattun bayanai, da kuma sauraren waƙoƙin da aka nazarta. A ƙarshen nazarin, wannan takarda ta ƙara tabbatar da wannan fahimta ta Shehin malamin na yadda marubuta waƙoƙin Hausa suke amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu, tare da sun sani ko ba su sani ba.

    Fitilun Kalmomi: Salo; Karin Magana; Abdullahi Bayero Yahya; Rubutattun Waƙoƙin


    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.004

    Download the article:

    author/Hussaini Hassan & Muhammad Musa Yankara

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages