Tsakure:
Harshe tamkar ɗan’adam ne domin kuwa, shi ma yana rayuwa kuma yana mutuwa. Harshe wani farashi ne da yake hauhawa a kasuwar duniya, kasancewarsa tubali da ya ɗaure duk wata al’ummar duniya ta hanyar yin mu’amala ko cuɗanya da juna. A wannan muƙala, an nuna yadda harshen Hausa,ya samu bunƙasa a duniya, sannan kuma da yadda yakan laƙume ƙananan harsuna, a inda sukan yi ɓatan-dabo, kasancewar yakan shiga lungu da saƙo har ya yi mamaya a nahiyoyi daban-daban na duniya. Hakan ta sa, ya bunƙasa kuma ya zama hantsi leƙa gidan kowa. Wannan ne, ya sa aka samu ra’ayoyin masana dangane da matsayinsa a yau. Binciken ya yi waiwaye dangane da wasu daga cikin ra’ayoyin masana a kan hakan. An yi amfani da hanyar tattara bayanai daga littafai da muƙalu da kundaye da ma intanet. Takardar ta hasko wasu kalmomin Hausa da sukan fuskanci barazanar ɓacewa ta fuskar cigaban zamani. Misali; matsefi – kum, kundi – albam, moɗa – kofi da sauransu. Daga ƙarshe, an bayar da shawarwari a kan yadda za a magance irin barazanar da harshen Hausa yakan fuskanta a wannan zamani, musamman wajen salwantar tsofaffin kalmomi da kuma salon tauye kalmomi masu tsawo dangane da sigarsu da yakan faru musamman a kafafen sada-zumunta daga wajen matasa.
Fitilun Kalmomi: Bunƙasa, Ɗorewa, Koma-Baya, Harshen Hausa, Duniya
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.045
author/Bashir, A. and Girei, I.I.
journal/GNSWH, April 2024