Wasu Matsalolin Kasuwanci a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato Jiya zuwa Yau

    Tsakure: 
    Wannan takarda tana magana ne a kan matsalolin kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato yadda suka faru da yadda suka kawo tarnaƙi da koma bayan tattalin arziki, ya kuma durƙusar da bunƙasar kasuwar. An gina wannan tunani ne bisa dalilin cewa har yanzu jama’a da dama ba su san irin matsalolin da kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato ta fuskanta a baya ba. Sakkwato tana babbar kasuwa da ake kira tsohuwar kasuwa da ke tsakiyar birnin mai ci a kowace rana. Manufar wannan takarda shi ne ƙoƙarin gano yadda wasu matsaloli suka jawo durƙushewa da rusa kasuwanci na wani lokaci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Don cimma manufar wannan aiki an bi hanyoyin tattara bayanai na hira da tattaunaa da wasu mutane mazauna tsohuwar kasuwa inda aka sami bayanai a kan yadda abubuwa suka yi ta faruwa, daga jama’a da hukuma da ƙungiyoyi daban-daban. Matsaloli kamar gobara da ambaliyar ruwa da matsalolin tituna da rashin tsaro da matsalar shugabanci da siyasa da banbance-babance tsarin tattalin arziki da yadda suka kawo naƙasu ga bunƙasar kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Sakamakon da binciken ya gano shi ne kowane al’amari na rayuwa na tattare da nasara da matsaloli iri daban-daban. Ita ma kasuwar Sakkwato ta fuskanci nasarori da matsaloli. Don haka wannan takarda ta keɓanta a kan matsalolin da kasuwar ta fuskanta a can baya da na yanzu. Hujja ita ce mafi yawan matsaloli irin na kasuwanci ɓoyayyu ne jama’a ba su cika ganin su a zahiri ba har sai an yi bincike.. 

    DOI: 10.36349/djhs.2026.v04i01.015

    Download the article:

    author/Ibrahim Alhaji Gado

    journal/Dundaye JOHS, July 2026

    Pages