Salo a Littafin Amon ‘Yanci na Halima Ahmad Matazu

    Tsakure: 

    Fagen nazarin salo, fage ne mai faxi wanda yake da buqatar a ci gaba da nazarta domin fito da hikimomi da zalaqar harshe da Allah ya albarkaci fasihai da marubuta na Hausa. Duk da cewa masana suna kallon fagen a matsayin wani fage da zai yi wahala a iyakance shi, saboda irin faxinsa (Xangambo 2007), hakan ba ya hana a iya hangen wasu abubuwa a kuma nazarce su a cikin wani matani. Wannan maqala ta yi nazari ne a kan salo a cikin littafin Amon ‘Yanci wanda Halima Ahmad Matazu ta rubuta. An yi amfani da hanyoyi nan kai-tsaye wajen nazarin, tare da bin hanyar nazarin salo ne ta fuskar adabi (Literary Stylistic), inda aka nazarci ‘ya’yan salo daga cikin wannan littafi. Daga cikin ‘ya’yan salo da bincike ya nazarta sun haxa da salon siffantawa, wanda ya qunshi kamance na daidaito da kuma na fifiko. Sai Salon jinsintarwa wanda ya qunshi mutuntarwa da kuma alamci. Haka kuma an nazarci salon aron kalmomi da amfani da tsofaffin kalmomi. Sannan an nazarci salon amfani da sassan adabin baka, inda a qarqashin haka aka nazarci karin magana a cikin matanin littafin. Maqalar ta yi amfani da hanyar bincike ce ta nazari na qwaqwaf, inda aka karanta litattfin tun daga shafin farko har zuwa na qarshe (1-300), tare da auna yawan layuka (7,800) da yawan sakin layi (900) da yawan kalmomi (70,200) da kuma yawan harufan (44,226,00) da marubuciyar ta yi amfani da su a cikin littafin. A qarshe binciken ya gane cewa marubuciyar ta yi amfani da ‘ya’ayan salo guda biyar a  cikin labarin nata. 

    Muhimman Kalmomi: Salo, ‘Amon ‘Yanci’ Halima Ahmad Matazu.  

    DOI: 10.36349/djhs.2026.v04i01.006

    Download the article:

    author/Rabiu Bashir, PhD and Abdullahi, Mujaheed

    journal/Dundaye JOHS, July 2026

    Pages