Abstract:
Sunan wannan maƙala shi ne nason kirari a waƙoƙin baka: nazari a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Danba'u Gidan Buwai. Manufar maƙalar ita ce nazarin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai tare da fito wa da baiwa da hikimomi da zalaƙar harshe da Allah ya ba shi wadda yake amfani da su wajen sarrafa kirari a cikin waƙoƙinsa. An gudanar da binciken ta hanyoyi daban-daban, waɗanda suka haɗa da tattaunawa da abokan hulɗarsa, musamman waɗanda suke taimaka masa, da kuma duba littattafai da kundin waƙoƙi. An kuma ziyarci gidajen rediyo da talabijin kamar Rima Radio, Rima TV, da NTA Sokoto don tattara bayanai. An dora binciken ne bisa ga littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau mai taken Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Sakamakon bincike ya nuna akwai Kirari mai yawa a cikin waƙoƙin nasa.
