Tsakure:
Kamar yadda taken ya nuna, “Mamayar Harshe a Nijeriya: Nazari a kan harshen Karai-Karai da Huasa” Manufar ita ce tunatarwa da jan hankali ga hukumomi da jagororin harshen kan yadda Hausa ta mamaye harshensu. Baya ga haka, ta yi amfani da lurar gani-da-ido da rubutattun bayanai da tattaunawa da mutane goma sha ɗaya a matsayin hanyoyin tattara bayanai domin samun ingantattun bayanai. An ɗora wannan aiki a kan ra’in Phillipson, R.L (1992) ra’in Babakeren Harshe (Linguistic Imperialism). Haka nan, takarda ta bayyana dalilai da suka haifar da babakeren. Daga cikin dalilai da suka haifar da babakere akwai rashin koya wa yara harshen uwa da halin ko oho dangane da harshen uwa da tasirin addini da auratayya da wayewa ko ƙauyanci na rashin amfani da harshen uwa da rashin koyar da harshen al’umma a makarantu da rashin amfani da harshen wajen gudanar da taruka. Har wa yau, takarda ta bayar da shawarwari kan iyaye su riƙa koya wa yara harshensu da amfani da harshen al’umma wajen gudanar da taruka da koyarwa a makarantu da sanya kishin harshen uwa ga yara da sauransu. Daga ƙarshe, sakamakon bincike ya nuna Hausa ta mamaye harshen Karai-Karai da kaso sittin (60%), Ke nan za a iya cewa harshen ya ɗauko hanyar ɓacewa wanda za ta iya kai shi ga mutuwa matuƙar mahukunta da jagororin harshen ba su ɗauki matakan kariya da suka dace ba,
Muhimman kalmomi: harshe, babakere, Hausa, Karai-Karai, amfani
DOI: 10.36349/djhs.2026.v04i01.002
author/Ishaku Abubakar, PhD and Hajjagana Adamu Jannare
journal/Dundaye JOHS, July 2026
