Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya: Keɓaɓɓen Nazari Kan Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Garba Maitandu

    Tsakure: 

    Waƙoƙin ɗarsashi ko rinjayen zuciya, waƙoƙi ne da kan wanzu a sakamakon wani abu da ya motsa wa mutum rai, da ya danganci farin ciki, ko farin rai, ko akasin haka, wato bakin ciki. Waƙoƙin ɗarsashin zuciya sun ƙunshi bayyana farin ciki ko bakin ciki bisa wani abu da ya faru ga mutun ɗaya ko ƙungiya wasu mutane, ko gari ko ƙasa (Gusau, 2008).Wannan maƙala za ta zaƙulo mabuɗin turken waƙoƙin ɗarsashin zuciya na Alhaji Garba Maitandu. Manufa a nan ita fito wa da mabuɗin turken waƙoƙin Garba Maitandu, wato in da aka fito da turken a bayyane. Duk abin da zai biyo bayan wannan mabuɗin turke tamkar warwarar turke ne da ake yin amfani da ƙananan tubalai domin gina babban turke.

    Fitilun Kalmomi: Mabuɗi, Turke, Ɗarsashin Zuciya, Waƙoƙin baka, Garba Maitandu

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.057

    Download the article:

    author/Shinkafi, R.H. and  Ibrahim, A.A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages