Gudummawar Habaici ga Gyara Halaye da Dabi’un ‘Yan Siyasa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Siyasa

    Tsakure: 

    Shugabanci wani jagoranci ne na jama’a na kowane nau’i, wato na gargajiya da na siyasa. Wannan muƙala mai take gudummawar habaici ga gyara halayen yan siyasa : Tsokaci kan wasu waƙoƙin siyasa.Manufar wannan muƙalar ita ce ta tattauna kan miyagun ɗabi’un ‘yan siyasa na rashin cika alƙawari da yaudarar alumma da ƙarya da hainci da zalunci da rashin adalci da sauransu. Shugabanci abu ne mai buƙatar mutane masu gaskiya da riƙon amana da sauran kyawawan ɗabi’u waɗanda za su taimaka a sami mulkin adalci a cikin al’umma. Zaman lafiya da cigaban tattalin arzikn ƙasa ba su samuwar sai shugabanni sun yi adalci a mulkinsu.Makaɗa da mawaƙan Hausa musamman na siyasa suna amfani da habaici a cikin waƙoƙinsu, domin su jawo hankalin alumma su gyara miyagun ɗabi’unsu kafin su shigo neman muƙami a siyasa.Zaɓen mutane nagari masu gaskiya da riƙon amana da cika alƙawari shi ke kawo cigaban ƙasa.. Habaici wani salo ne na isar da saƙo ga alumma ta hanyar yi wa yan siyasa gargaɗi da haska masu fitila domin su gyara kurakuransu da ɗabi’unsu, muddin suna son a zaɓe su, su wakilci al’ummarsu a gwamnatin farar hula.Wannan maƙala za ta mai da hankali ne ga nazarin rawar da habaici yake takawa wajen gyara miyagun halaye da ɗabi’un ‘yan siyasa, waɗanda suka dabaibaye siyasar zamani, suka hana ci gaba a Nijeriya. Amfani da habaici da mawaƙa irin su Aminu Alan Waƙa da Ibrahim Yala da Dauda Kahutu Rarara da sauransu suka yi a cikin waƙoƙinsu ya taimaka wa yan siyasa wajen gyara ɗabi’u da halayensu kafin su shiga fafatakar neman kowane irin muƙami a siyasa. An ɗora wannan bincike bisa ra’in  makisanci, wanda ya nuna cewa ya kamata adabi ya kasance makami na siyasa, kuma makamin gabatar da ci gaba. Sannan adabi ya bayyana fasaha da muryar  talakawa, wato ya kasance bangare na siyasa, (Lenin 1905).

    Fitilun Kalmomi: Habaici, Gyara Halaye, Dabi’u, ‘Yan Siyasa, Waƙoƙin Siyasa

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.056

    Download the article:

    author/Aliyu Rabi’u Dangulbi

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages