Tsakure
Hausawa al’umma ce mai tsananin riƙo da al’adunsu na gargajiya, musamman abubuwan da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa da sutura da bukukuwa da sauran al’adun da suka keɓance su ta fuskar zamantakewa. Manufar wannan takarda ita ce, a bibiyi wasu sassan al’adun Hausawa na gargajiya a littafin Gumakan Zamani wallafar Yusuf M. Adamu. Ta haka ne aka lalubo ɗimbin al’adu da suke ɗamfare a labarin kamar; tsarin shugabanci da sana’a da aure da cimaka da karimci da yanayin zamantakewa. An ɗora wannan bincike a bisa ra’in Gudummuwar Adabi ga Al’umma (Functional Theory), wanda yake duba yadda aikin adabi yake tafiya da al’adu na al’umma da yadda suke daɗa inganta rukunonin rayuwa. Hanyoyin tattaro bayanan wannan aiki sun haɗa da; nazartar littafin Gumakan Zamani sau da ƙafa da zimmar kalato wasu al’adun Hausawa. An yi bitar ayyukan magabata masu alaƙa kamar; wallafaffun littattafai da kundayen bincike da maƙalu da sauran takardu na ilimi. Binciken lura cewa, mawallafa ƙagaggun labarai na Hausa suna amfani da hikima wajen sakaɗa hoton al’adun Hausawa a littattafansu. Ta haka ne kuma, labaran nasu suke taka muhimmiyar rawa wajen rayawa da taskace al’adun gargajiyar Bahaushe.
Fitilun Kalmomi: Ƙagaggen labari, Al’ada, Adabi, Hausawa, Gargajiya
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.069