Adon Harshe a Waƙar Kirmau Uban Gabasawa ta Aminu Ladan (Alan Waƙa)

    Tsakure 

    Kiɗa da waƙa abubuwa ne da zai yi wuya a raba Bahaushe da su. Hausawa suna amfani da waƙa wajen faɗakarwa ko wa’azantarwa ko yabo musamman a fada. “Abun da wuya wai gurguwa da auren nesa” a raba fada da makaɗa. Wannan takarda mai taken “Adon harshe a waƙar Kirmau Uban Gabasawa” ta bibiyi wasu daga cikin adon harshe da makaɗa Aminu Ala ya yi amfani da su a cikin waƙar. Masana da manazarta kamar Gusau (2014) da Ɗanbappa (2019) sun nazarci adon harshe a fannonin adabi daban-daban. Fannonin sun haɗa da, jawabai na shugabanni da waƙoƙi a matsayin dabarun jawo hankali da sa karsashi. An yi amfani da ra’in Gusau ( 2008 ). Hanyoyin da aka bi domin gudanar da bincike sune ta sauraron waƙar da kuma bibiyar masana da litattafai da maƙalu domin gano irin adon harshen da aka yi amfani da su a waƙar. An gano yadda Makaɗa Ala ke amfani da ƙwarewar harshe wajen zaƙulo kalmomi cikin hikima domin waƙa ta zama mai sa karsashi da armashi. Makaɗa Ala ya yi amfani da adon harshe na siffantawa da mutuntawa da dabbantawa da abuntarwa da kambamar zulake. 

    Fitilun Kalmomi: Adon Harshe, Waƙar Kirmau Uban Gabasawa, Aminu Ladan (Alan Waƙa)

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.068

    Download the article:

    author/Ali, B.Y. and Danbappa, H.R.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages