Tsakure
Wannan maƙala mai taken “Baramu hanyar Neman Arziki: Tsokaci daga wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo” ta fito da tasirin sana’ar baramu ne a kan sauran sana’o’i, tamkar yadda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi ishara da su a wasu waƙoƙinsa. A wannan makala an mayar da hankali ne a kan wasu daga cikin waƙoƙin Ɗankwairo waɗanda suka haɗa da: Waƙar ‘Yan Arewa da ta Alhaji Bala Ɗan Umaru da ta Gojen Noma Ɗan Musa, wajen zaƙulo alfanun da baramu suke da shi a wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma da ƙasar Hausa baki ɗaya. An yi amfani da ingantattun dabarun bincike waɗanda suka haɗa da ziyartar ɗakunan karatu, inda aka nazarci wasu ayyuka da aka gabatar a kan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairao. Sannan aka bibiyi ɗakin adana fasahar baka na Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, da kuma sauraren MP3 da CD-CD, sannan aka zaƙulo wuraren da wannan fasihi ya ambaci tarihin waɗannan baramu da tasirinsu ga rayuwar Hausawa ta fuskar ci gaban tattalin arziki. Haka kuma, maƙalar ta gano cewa, sana’ar baramu tana da tasiri a kan sana’ar siminti da sarrafa ƙarfen tama da sarrafa fatu da ƙiraga da sarrafa kayan ƙyale-ƙyale da kuma sana’ar gine-gine, duk sun dogara ne a kan sana’ar baramu. A ƙarshe binciken ya gano cewa, Alhaji Musa Ɗankwairo yana daga cikin shahararrun mawaƙa da suka fito da muhimmancin baramu ta fuskar haɓakawa da ci gaban tattalin arziki a ƙasar Hausa.
Fitilun Kalmomi: Baramu, Neman Arziki, Waƙoƙin Baka, Alhaji Musa Ɗanƙwairo
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.071