Ɓurɓushin Sana’ar Sassaƙa a Wasu Waƙoƙin Baka Na Hausa

    Tsakure

    Sana’ar sassaƙa wata muhimmiyar sana’a ce da aka daɗe ana aiwatarwa a ƙasar Hausa, kuma ta taimaka sosai wajen samar da kayayyakin ayyuka da amfanin jama’a na yau da kullum. Duk da haka al’umma tana yi wa sana’ar sassaƙa riƙon sakainar kashi. Wannan shi ya jawo hankalina, na rubuta wannan maƙala. Manufar wannan maƙala ita ce ƙoƙarin nazarin ɓurɓushin sana’ar a bakin wasu mawaƙan Hausa. A nan, maƙalar ta yi nazarin wasu zantuka da mawaƙan kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu da suka shafi sana’ar sassaƙa kai tsaye ko kaikaice. An ɗauki hanyar nazarin waƙoƙi da tattaunawa a matsayin dubarun aiwatar da wannan bincike. An ɗora akalar wannan bincike a kan tunanin Bahaushe da ke cewa, “Kowani gauta ja ne, sai wanda bai ji rana ba”. Dalilin ɗora wannan maƙala a wannan Bahaushen tunani shi ne ganin cewa, wasu jama’a na yi wa wannan sana’a kallon hadarin kaji tamkar wadda aka bar yayinta saboda shigowar wasu kayayyakin zamani. Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, samuwar ɓurɓushin sassaƙa a cikin waƙoƙin Hausa ya ƙara jaddada matsayi da muhimmincinta a rayuwar Hausawa.

    Fitilun Kalmomi: Sana’a, Sassaƙa, Waƙoƙin Baka

    Download the article:

    author/Rabiu Aliyu Rambo

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages