Tsakure:
Wannan takarda ta ƙunshi tsokaci ne, ko nazari kan yadda Aminu Ladan Abubakar ALA ya sarrafa wasu zantuttuka da kalmomi masu alaƙa da ɗarsashin zuci cikin wasu waƙoƙinsa. Mawaƙin ya sarrafa zantuttuka da dama, domin faɗakarwa da ilmantarwa ko wa’azantarwa a kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum. Batutuwa masu alaƙa da ɗarsashin zuciya, batutuwa ne da suka faru ba wai shaci faɗi ba, waɗanda suke sosa zuciyar mawaƙin a duk lokacin da suka faɗo masa rai, ko suka motsa masa zuciya. Har wa yau kuma batutuwa ne da suke riƙe a zuciyar mawaƙin yake ganin ba zai iya mantawa da su ba a rayuwa. A taƙaice dai manufar wannan nazari shi ne fito da tasiri da muhimmancin ire-iren waɗannan zantuttuka da kalmomi, waɗanda mawaƙin ya sarrafa a cikin waƙoƙinsa. An yi amfani da ɗiyoyin waƙoƙin mawaƙin a inda aka tattara bayani da suka shafi ɗarsuwan zuci, wanda a ƙarshen binciken an gano cewa sarrafa ire-iren waɗannan zantattuka masu alaƙa da ɗarsashin zuci a waƙa, suna da tasiri da muhimmanci domin kusan duk abubuwan da mawaƙin yake ambatawa a waƙar, tabbatattu ne wato sun faru a zahirance, ba wani shaci faɗi ba ne..
Fitilun Kalmomi: Ɗarsashin Zuci, Waƙoƙi, Aminu Ladan Abubakar
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.052
author/Garba Lawal
journal/GNSWH, April 2024