Nazarin Tsarin Sautin wasu Kalmomin Hausa na Aro a Harshen Bade

    Tsakure: 

    A duk lokacin da mutane suka haxu wuri guda da nufin cuxanya/mu’amala. Ya zama tilas su yi amfani da harshe domin cim ma wata manufa ta rayuwa. Zavan harshe hulxa yayin cuxanya ko mu’amala kuwa tilas ne. Are-aren kalmomi a wannan yanayin ya zama wajibi ya bayyana. Musammam ma daga harshen da aka zava a matsayin harshen hulxa. Takardar ta fito da yadda harshen Hausa ya yi tasiri a kan harshen Bade har ta kai ga yana aron kalmomi daga Hausa. Sakamakon bincike ya bayyana yadda kalmomin Hausa na aro ta fuskar tsarin sauti, ke taka rawa a harshen Bade. Ga misali ganxantaccen bahanxe a Hausa na canjawa ya koma baganxe a sanadiyar aro a harshen Bade. Kazalika aron na haifar da bahanqe marar ziza yana komawa bahanqe mai ziza musamman a tsakiyar kalma. Har ila yau, ana samun shafe wasali a qarshen kalmar Hausa idan an are ta a harshen Bade. Ga misali Kalmar mizani a daidaitacciyar Hausa tana komawa mizan a furucin Badawa a sanadiyar aro. Haka kalmarhankali a Hausa tana komawa hankal a furucin Badawa. Tambayoyi da hirarraki a tsakanin mutanen Gashuwa da lura a fakaice na daga cikin hanyoyin da aka bi domin tattara bayanan wannan nazari. Aikin an xora sa a kan Ra’in Cuxanya (Contact Theory) da na Rarrabewar Sauti (Distinctive Features Theory) na Chomsky da Hally domin fito da manufar binciken a sarari. Ana sa ran nazarin zai zamo alfanu ga manazarta walwalar harshe da sauran rassan harshen a jumlace.  

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.013

    Download the article:

    author/Abubakar Babangida & Abdullahi Yakubu Darma

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages