Tsakure:
Wannan takarda ta yi nazarin wasu kalmomi da harshen Hausa ya ara daga harshen Larabci, waɗanda Malaman zaure ke amfani da su a yayin karatukansu a zaure ko majalisi a masallaci. Wannan takarda ta fito da waɗansu misalai da aka fi yawan jin Malaman zaure ke yawan furtawa a lokacin karantarwarsu, tare da tasirin karin harshen Yamma. Haka kuma an ɗora wannan takarda kan ra’in hulɗa tsakanin harsuna wanda Greenberg (1962) ya yi amfani da shi. An tattara waɗannan bayanai ta hanyar zama a majalisin karatu zaure da masallaci da sauraren karatukan waɗansu malamai na zaure, da kuma waɗansu ayyukan da aka wallafa masu alaƙa da wannan bincike. Samakon nazarin ya tabbatar da cewa: (i) Ana samun aro na kaitsaye ta fuska uku; (a) aron lafazi da ma’ana sukutum; da (b) aron lafazi ban da ma’ana da kuma (c) aro da faɗaɗa ko karkatar da ma’ana. (ii) takardar ta lura da ana samun tasirin shaddantawa a mafi yawan Hausar Malaman zaure na Sakkwato da Kabi.
DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.015
author/Buhari Atiku Gwandu
journal/Dundaye JOHS, December 2025
