Hausa a Potiskum: Nazari ta Fuskar Kirar Kalma

    Tsakure: 
    Kamar yadda taken yan nuna “Hausa a Potiskum: Nazari ta fuskar kimiyyar harshe” takarda ta bayyana yadda al’ummoin Potiskum suke tasrifin kalmomin Hausa. Sannan, takarda ta yi amfani da tattaunawa/hira da lurar gani da ido da yanar-gizo da rubutattun bayanai a matsayin hanyoyin tattara bayanai. Baya ga haka, ta yi amfani da Aronoff, M. (1976) Ra’in Gina Kalma daga Kalma (Word Based Theory). Sakamakon bincike ya nuna al’ummomin Potiskum suna amfani da shafe sauti da ɗafa goshi da ɗafa ciki da ɗafa ƙeya a matsayin hanoyin ginin kalma.  

    DOI: 10.36349/djhs.2025.v03i02.008

    Download the article:

    author/Ishaku Abubakar

    journal/Dundaye JOHS, December 2025

    Pages