Tsakure:
Manufar wannan bincike ita ce, fayyace irin gudummuwar da marubuta waƙoƙin siyasa suka bayar wajen bunƙasar siyasar jam’iyyu a Nijeriya. An yi amfani da sharhantaccen bincike (Qualitative Method) wajen gina wannan aiki. Haka kuma, an ɗora wannan bincike a kan ra’in muhimmancin Rubutacciyar Waƙa, (Theory of Appreciation on Hausa Written Poetry) wanda Farfesa Ɗangambo (2007) ya assasa, musamman ɓangaren da ya yi magana a kan jigo da hanyoyin binciko manya da ƙananan jigogi a Rubutacciyar waƙa.Da kuma salo da sarrafa harshe.A wajen tattaro bayanan wannan bincike, an yi amfani da hanyoyi da dama waɗanda suka haɗa da; ziyartar marubuta waƙoƙin siyasa. Da tattaunawa da su domin jin bayanin yadda suka ɗauki waƙoƙin siyasar jam’iyyu. An yi bitar matanin waƙoƙin a rubuce domin a samu damar ƙalailaice jigon siyasa a cikinsu. Binciken ya gano cewa da yawan marubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu na ƙasar Hausa, sun fi shahara a kan abin da ya shafi siyasar aƙida, a wasu lokutan sukan yi amfani da dabarun jawo hankalin masu sauraron waƙoƙinsu wajen yin karin magana da zambo da habaici domin kushe abokan adawar siyasa, da kushe jam’iyyarsu duk domin masu zaɓe su ƙaurace mata, da kuma cusa musu ra’ayin riƙau na kishin jam’iyya da rashin tsaro a kan duk abin da ya taso. A ƙarshe binciken ya gano cewa, marubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu sukan yi amfani da salon kamantawa da kwatantawa da siffantawa da jinsintarwa da mutuntarwa da dabbantarwa dakambamawa da alamtarwa duk a cikin waƙoƙinsuna siyasa. Haka kuma, binciken ya lura da wasu Jigogi da su keamfani da su. Irin waɗannan jigogi sun haɗa da na yabo da zuga ta hanyar bayyana manufofin jam’iyyu da na tallata ayyukan raya ƙasa na gwamnati..
Fitilun Kalmomi: Waƙoƙin siyasa, Jam’iyyu, Jigo, Salo, Nijeriya
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.059
author/Yunusa Ibrahim Adamu
journal/GNSWH, April 2024