Waƙaƙƙen Aruli: Nazari a Bisa Bahaushen Kari Tare da Ƙafafuwansa Don Ƙwaƙulo Aruli na Hausa

    Gabatarwa

    1. Manazarta ai nazari kan waƙa,
    Domin nazari kan ma’aunin waƙa,
    Shi ne ginshiƙin kimiyyar waƙa.

    2. Ma’aunin waƙa shi ke bambanta zube,
    Idan ko an yo taliyo har gobe,
    Aruli shi ne nahawunmu na waƙa.

    3. Idan ko waƙa ta ƙi amsa Aruli,
    Tilas masana ku ji wannan ƙauli,
    Mafita dai gun Malamanmu na waƙa.

    4. Cikin biyu dai dole a samo mafita,
    A samo hujja wadda ta inganta,
    Na tantance ƙafafu na wannan waƙa.

    5. Marubucin waƙa ya samar baiti,
    Shi mai nazari shi yake li’irabi,
    Ya sanya ƙafafu kan gaɓoɓin waƙa.

    6. Idan sun karɓa sunyi kan-kan-kan to,
    A dukka karorin sun yi riga da gyauto,
    Aruli ya inganta wannan waƙa.

    7. A dukka karorin fa idan sun ƙi su hau,
    Cikin biyu tabbas ba guda wanda ya hau,
    Ku ce musu zance bai zame war waƙa.

    8. Muna da ma’auni kan zuwan Larabawa,
    Arulinmu yana nan na ‘yan Hausawa,
    Da shi ne muka tantance dukkan waƙa.

    9. Saninsa muhimmi ne ga duk mai nazari,
    Ya gane waƙa take, yanke sarari,
    Shi ne ya bambance Ƙur’ani da waƙa.

    10. Kowane ilimi na da amfaninsa,
    Ka bar ma’abutansa su je nazarinsa,
    Ilimin ya zamto ribaɗin waƙa.

    11. Ga dukka gudanmu wanda ya yi wakilci,
    Mu mar son barka ya tsare mana ‘yanci,
    A kan wannan fannin kimiyyar waƙa.

    12. Idan kuma ba ɗai a cikin al’umma,
    Da za yai magana gwargwado ma dama,
    A bisa Aruli don kimiyyar waƙa.

    13. Masana ku fahimta da sauran aiki,
    Ku faɗaɗa ilimi don ku kawo ɗauki,
    A kan bigiren nan na Arulin waƙa.

    14. Masha Allah yanzu kam mun dace,
    ‘Ya’yan Hausawa a yau sun ƙwace,
    Suke ta rubutun Arulin waƙa.

    15. Masana da yawa sun wuce ai gwalo,
    Irin su Galadanci da Sheshi da Bello,
    Sun yi rubutu kan Arulin waƙa.

    16. Magabata sun yi rubutu da yawa,
    Irin su ubana Baba ɗan Dunfawa,
    Da ya ba ni karatun Arulin waƙa.

    17. Don haka ne na ɗauki alƙalamina,
    In tofa ɗan albarkacin bakina,
    Don in yi waƙaƙƙen Arulin waƙa.


    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.012

    Download the article:

    author/Alhaji Ibrahim

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages