Tsakure:
Waƙa wata fasaha ce da Allah ya hore wa ɗan’Adam wajen amfani da harshensa da tunaninsa, domin ya isar da saƙo ga al’ummar da yake a cikinsu. Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da nau’o’in mawaƙa da makaɗa da dama, musamman a yankin Sakkwato da Zamfara da Kabi. Wannan yankin ciki yake da fitattun mawaƙa da makaɗa na fannonin rayuwa daban-daban. Misali akwai Ibrahim Narambaɗa da Salihu Jan kiɗi da Sa’idu Faru da Aliyu Dandawo da Sani Aliyu Dandawo da kuma Alhaji Abdun Inka Bakura da suka yi fice a waƙoƙin sarauta. A ɗayan ɓangaren kuwa akwai Alhaji Musa Dankwairo Maradun da ya shahara a waƙoƙin Jama’a, kazalika akwai Alhaji Dan’Anace da ya shahara a fagen waƙoƙin maza (Dambe). Amali Sububu kuwa ya yi fice ne a waƙoƙin noma. Basirar da waɗannan makaɗa da mawaƙa suke da ita ba ƙarama ba ce. Gane irin wannan basirar kuwa ba zai yiyu ba, sai an koma ga fahimtar yadda suke ƙulla zaren tunaninsu musamman ta amfani da salailai masu armashi da burgewa. Nazari ya yi nisa game da waƙoƙin waɗannan mawaƙa, sai dai ba a zurfafa bincike ba dangane da salon aiwatar da waƙoƙinsu a ɗaiɗaikun mataki, face kaɗan daga cikin manazarta da suka aiwatar da irin wannan nazari (Dankwairo, 2019). Maƙasudin wannan maƙala shi ne domin a yi nazarin irin yadda makaɗa Abdun Inka Bakura yake turke ɗiyan waƙoƙinsa da yabon nasaba da kuma duba yadda suka mamaye wasu daga cikin waƙoƙinsa. Dabarun da aka bi wajen gano hakan kuwa shi ne ta amfani da sauraren waƙoƙinsa da aka naɗa a kaset-kaset da C.D da kuma wayoyin zamani. Daga ƙarshe takardar ta tantance da kuma gano yadda yabon nasaba ya mamaye sauran salailai da ke cikin waƙoƙin Abdun Inka Bakura da yadda kutsen salon ke ƙara ƙawata waƙoƙinsa. Takardar ta gano cewa da za a cire yabon nasaba a cikin waƙoƙinsa, da waƙoƙinsa ba su sami gindin zama ba.
Fitilun Kalmomi: Turke, Nasaba, Waƙoƙin baka, Abdun Inka Bakura
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.020
author/Abdullahi Sarkin Gulbi & Umar Ahmed
journal/GNSWH, April 2024