Tsakure:
Hausawa na cewa “zaman lafiya mai daɗi”. Tatsuniya tana daga cikin fannonin adabi da suka game duniya baki ɗaya, saboda a kowane harshe da ke cikin faɗin duniya komai ƙanƙantarsa da rashin yawan masu amfani da shi ana samun tatsuniya a cikinsa. (Dorson 1972 a cikin Koko 2009). Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu tatsuniyoyin Hausa a yi fashin baƙinsu dangane da saƙon zaman lafiya da suke ɗauke da shi. Saboda haka, takardar ta fito da wasu ginshiƙan samar da zaman lafiya da ke cikin wasu tatsuniyoyin waɗanda suka haɗa da riƙon amana da adalci da haƙuri da alkawali da yafiya da kuma haɗin kai don a gudu tare a tsira tare.
Fitilun Kalmomi: Gudunmuwa, Zaman Lafiya, Tatsuniya
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.022
author/Musa Shehu & Lauwali Aliyu
journal/GNSWH, April 2024